29 Disamba 2025 - 22:21
Source: ABNA24
Araqchi: Shahid Suleimani Ya Tabbatar Da Cewa Gwagwarmaya Wata Dabara Ce Mai Tasiri Ga Ƙasashe Masu Mutunci

Sayyid Abbas Araqchi ya ce Shahid Qassem Suleimani ya tabbatar da cewa Gwagwarmaya "zabi ne mai mahimmanci" kuma hanya ce kwara daya tilo mai kyau ga kasashe waɗanda ke fifita mutuncinsu fiye da komai.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Ministan Harkokin Wajen Iran Sayyid Abbas Araqchi ya bayyana Shahid Janar Qassem Suleimani a matsayin wanda ya gina ginshiƙin gwagwarmaya a yankin, yana mai cewa, "Shahidi Suleimani ya tabbatar da cewa gwagwarmaya wata zaɓin salone kuma dabara ce ga ƙasashe masu fafutukar samun mutunci".

A jawabinsa a buɗe taron ƙasa da ƙasa mai taken "Diflomasiya da Gwagwarmaya A Mahangar Shahid Qassim Sulaimani" Ministan Harkokin Waje Abbas Araqchi ya yi nuni ga tushen ilimi da tunani na Janar Suleimani, yana mai cewa tunanin Janar Suleimani ya ƙunshi tushen juyin juya halin Musulunci kuma ya dogara ne akan akida da tushe na manufofin siyasar cikin gida da ta waje wanda ya kamata a kira shi diflomasiya bisa tushen Gwagwarmaya.

Ya ƙara da cewa rawar da sassan ikon ƙasa ke takawa tana da matuƙar muhimmanci ga nasarar diflomasiya saboda diflomasiya maras tushe ba ta kawo fa'idodi da yawa ba. Ministan Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa Janar Suleimani ya 'yantar da akidar gwagwarmaya daga take-take da ra'ayoyi, inda ya mayar da ita wata babbar runduna mai tasiri ga sauyi a yankin Gabas ta Tsakiya da Yammacin Asiya mai cike da rudani.

Ya tabbatar da cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta ci gaba da goyon bayan diflomasiyyar Gwagwarmaya da kuma akidarta.

Sayyid Abbas Araqchi ya ce Shahid Qassem Suleimani ya tabbatar da cewa Gwagwarmaya "zabi ne mai mahimmanci" kuma hanya ce kwara daya tilo mai kyau ga kasashe waɗanda ke fifita mutuncinsu fiye da komai.

Your Comment

You are replying to: .
captcha